Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a sashin shari’a na karamar hukumar Ikot Ekpene a jihar Akwa Ibom ta yankewa wani matashi dan shekara 25, Idorenyin Udoh Umoh, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 17 fyade.
Acewar takardun kotun, tun a watan Mayun 2022 ake shari’a da matashin kan laifin yi wa yarinyar fyade a karamar hukumar Ikot Ekpene.
- Mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai: Tsakanin Barau Jibrin Da Saura
- Yadda Wasu ‘Yan Mata Ke Yawan Kai Ziyara Wurin Saurayi Da Gidan Surukai
Mai shari’a Charles Ikpe ya samu matashin da laifi inda ya yanke masa hukunci a karshen mako.
Mai shari’a Ikpe ya kuma sake samun matashin da laifin cin zarafi inda ya kara yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu daban a gidan yarin.