Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi ma’aikatansa da su yi aiki da gaskiya wurin gudanar da zaɓen gwamnoni da za a yi a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa a ranar Asabar mai zuwa.
Yakubu ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da ya kai wata ziyara don tabbatar da irin shirin da aka yi wajen gudanar da zaɓuɓɓukan a jihohin.
- Tinubu Ya Jajanta Wa Gwamnatin Canada Kan Gobarar Da Ta Tashi A Ofishin Jakadancinta
- Yadda Mahara Suka Kashe Mutane Da Sace Wasu Da Dama A Wurin Maulidi A Katsina
Shugaban ya tabbatar da cewa, za a biya dukkan ma’aikatan dukkan alawus ɗin su kafin a fara zaɓen.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ke ɗauke da rahotannin aikace-aikacen INEC na yau da kullum, wadda hukumar ke wallafawa.
Yakubu ya ƙara da cewa, INEC ta himmatu sosai wajen wanzar da ingantacce kuma sahihin zaɓe a jihohin uku.
Ya ce: “INEC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kuma ba ta da wani ɗan takara daga cikin masu takarar gwamnan.
“Abin da za mu tabbatar shi ne, mu himmatu domin tabbatar da gudanar da zaɓen da zai gamsar da jama’a, cewa, mutane sun zaɓi wanda su ke so. Kuma da ma nauyin da ya rataya a wuyanmu shi ne mu kare dukkan abin da jama’a suka zaɓa.”