• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gargaɗin Amurka Kan Nijeriya Na Tada Hankulan Masu Zuba Jari A Kasar – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Amurka

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gargaɗin da Amurka ta fitar kan Nijeriya ya na kawo babban cikas ga tattalin arzikin ƙasar.

Idris ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Litinin a Abuja.

  • Cin Zarafi: Kungiyoyin Kwadago Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Ranar 14 Ga Nuwamba
  • Ka Nemi Sana’a Siyasa Ba Taka Ba Ce,Tinubu Ga Peter Obi

A ranar Juma’a, 3 ga Nuwamba, Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar “wata babbar barazana” ga manyan otal-otal da ke faɗin Nijeriya, amma ya ce jami’an tsaron Nijeriya na aiki tuƙuru domin daƙile barazanar.

Idris ya ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne, kada a yi wa barazana fassara da cewa, ta mamaye dukkan faɗin ƙasar nan, domin yin hakan ba wani alheri ba ne.”

Amurka

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Ya ƙara da cewa, a kullum gwamnati ta na ɗaukar tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a da sauran dukkan maziyarta cikin ƙasar nan da muhimmanci.

Ya ce: “Mun fahimci damuwar da Amurka ke nunawa a cikin gargaɗin da ta fitar. Amma mun ga cewa, hakan bai kamata ba kuma bai dace a nuna wannan barazanar ta shafi dukkan otal-otal ɗin faɗin ƙasar nan ba.

“Abin da mu ka lura shi ne, yawancin wannan gargaɗin ba ya haifar da wani alheri, sai dai ya firgita mutane su tashi hankulansu. Sai kuma kawo illa ga tattalin arzikin ƙasa da gargaɗin ke yi. Sannan kuma ya kan zama wata hanyar yi wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samun masu zuba jari a cikin ƙasa zagon ƙasa.

“A kullum mu na bayar da fifiko wajen kare rayuka da lafiyar duk wasu baƙin da su ka kawo ziyara cikin ƙasar nan.”

Amurka

Minista ya kuma rufe taron da bayyana irin nasarorin da jami’an tsaro su ka samu wajen daƙile matsalar tsaro a wasu jihohin ƙasar nan daban-daban a ‘yan kwanakin nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima
Manyan Labarai

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
Fashewar Tankar Gas Ce Sanadin Tashin Gobara A Ofishin Jakadancin Canada – FEMA

Fashewar Tankar Gas Ce Sanadin Tashin Gobara A Ofishin Jakadancin Canada - FEMA

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.