Wata babbar kotun Abuja da ke zamanta a Maitama, a ranar Laraba, ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, CBN, Mista Godwin Emefiele da ake tsare da shi.
Kotun, a hukuncin da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta bayar da umarnin a sake shi zuwa ga lauyoyinsa.
- Da Ɗumi-ɗuminsa: EFCC Ta Gabatar Da Tsohon Gwamnan CBN A Gaban Kotu
- DSS Ta Saki Tsohon Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
“Dole ne a kawo karshen tsarewa ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.”
Kotun ta ce, ba za ta iya barin Emefiele ya ci gaba da zama a gidan yari sabida ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa, za ta gurfanar da shi a ranar 15 ga watan Nuwamba a kan wata sabuwar tuhuma.
Don haka, kotun ta bayar da umarnin a saki Emefiele ga wata tawaga ta manyan lauyoyin Nijeriya uku, SAN, wadanda suka wakilce shi a gaban kotun.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 2 ga watan Nuwamba mai shari’a Adeniyi ya umarci hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC da ta saki tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, ba tare da wani sharadi ba, ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu domin bayar da belinsa.
A bisa bin wannan umarnin, hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu domin sauraron bukatar bayar da belinsa.