Wata sanarwar da ma’aikatar kula da muhalli da muhallin halittu ta kasar Sin ta fitar a Alhamis din nan, ta ce an cimma nasarori yayin taron sauyin yanayi da ya gudana a jihar California ta Amurka tsakanin wakilan Sin da na Amurka.
An kammala tattaunawar ne dai a jiya Laraba, bisa jagorancin wakilin musamman na kasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, da wakilin musamman na shugaban kasar Amurka kan sauyin yanayi John Kerry. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp