Yawan kayayyaki da masu harkar isar da sako wanda aka fi sani da ‘masu dilibri” na kasar Sin suka yi jigilarsu ya kai wani matsayi mafi girma a lokacin bikin sayayya ta yanar gizo na “Double 11”, wanda ya gudana daga karshen watan Oktoba zuwa tsakiyar Nuwamba, a cewar hukumar kula da sakonni ta kasar a yau Lahadi.
Daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa 11 ga watan Nuwamba, kamfanonin jigilar kayayyaki a fadin kasar sun tattara jimillar kunshin kayayyaki biliyan 5.26, wanda ya karu da kashi 23.22 cikin dari daga shekarar da ta gabata, a cewar hukumar.
- Mataimakin Firaministan Sin Ya Gana Da Sakatariyar Baitul Malin Amurka
- Afirka CDC Ta Bude Dakin Gwaje-gwajen Bincike Da Sin Ta Samar
A ranar Asabar din da ta gabata, an tattara jimillar kunshin kayayyaki miliyan 639 a fadin kasar, inda hukumar ta kara da cewa adadin ya ninka sau 1.87 na adadin jigilar da aka saba yi, wanda ya karu da kashi 15.76 idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara.
Sana’ar isar da kayayyaki ta kasar Sin ta kara habaka, tana ba da gudummawa ga farfadowa da fadada kasuwannin kayan masarufi, kuma tana nuna cikakken karfin tattalin arzikin kasar Sin, a cewar hukumar. (Yahaya)