Rundunar sojojin Nijeriya ta ce dakarun rundunar ta daya sun halaka ‘yan bindiga uku tare da kwato makamai a Kaduna.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Sojojin Nijeriya, Laftanal Kanal Musa Yahaya, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutum 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
- An Kashe ‘Yan Bindiga Da Cafke 19 A Filato Da Kaduna
“Sojojin runduna ta daya ta sojojin Nijeriya tare da hadin guiwar ‘Operation Whirl Punch’ sun kai wani sumame a yankin dajin Maro – yanki a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Nuwamba.
“A yayin kai farmakin, sojojin sun fatattaki ‘yan bindigar da bakin bindiga, inda suka kashe daya daga cikin ‘yan bindigar tare da tilasta wa wasu tserewa zuwa dajin da ke kewayen yankin,” cewar rundunar.
Rundunar ta kuma ce sojojin sun kama bindigar kirar AK 47 guda daya da AK 47 kirar gida guda daya, alburusai na musamman 7.62mm da wayar salula daya.