Gwamnatin tarayya ta bayyana takaicinta kan matakin da Kungiyar Kwadago ta Nijeriya ta yanke na kiran ma’aikata da su tsunduma yajin aiki daga tsakar daren 13 ga watan Nuwamba duk da umarnin hana kungiyar tsunduma yajin aiki a makon jiya da Mai Shari’a Benedict Backwash Kanyip na Kotun Masana’antu ta Kasa ya bayar.
Wannan shawarar da NLC da TUC suka yanke, yunkuri ne na yi wa gwamnatin zagon kasa kuma wannan sam ba abun lamunta ba ne.
- Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Yajin Aikin Da Za Mu Shiga – NLC
- Kungiyar Kwadago Ta Tsunduma Yajin Aiki Yau Talata
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar yayin da yake mayar da martani kan fara yajin aikin da kungiyar ta soma.
“Har yanzu mun rasa dalilin da ya sa NLC da TUC suka yanke shawarar hukunta daukacin kasar nan mai mutane sama da miliyan 200 kan wani lamari na kashin kai da ya shafi shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, wanda kuskuren hukuncin da ya yanke ne ya janyo masa hakan a Owerri a yayin da ya ke shirin tunzura ma’aikata a jihar Imo tsunduma yajin aikin da bai kamata ba.
“Yayin da gwamnatin tarayya ba ta lamunci duk wani nau’i na tashin hankali da cin zarafi ga kowane dan Nijeriya ba duba da tsare mutuncin zamantakewa da harkokin tattalin arzikin kasa, nan ta ke Sufeto Janar na ‘yansanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya faru da Mista Ajaero yayin da Kwamishinan ‘yansanda na jihar Imo wanda lamarin ya faru a karkashinsa aka sauya masa wurin aiki zuwa wajen jihar.”