Daga ranar 14 zuwa ta 17 ga watan da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai je birnin San Francisco na kasar Amurka, don ganawa da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, bisa gayyatar da aka yi masa, kana zai halarci taron kwarya-kwarya karo na 30 na shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yankin Asiya da na tekun Pasific (APEC).
Yanzu haka, an riga an kafa wata cibiyar watsa labarai ta babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG) a San Francisco, inda wasu ’yan jarida fiye da 180, daga rassan CMG dake Beijing na kasar Sin, da arewacin nahiyar Amurka, da MDD, da reshen CGTN dake arewacin nahiyar Amurka, sun riga sun isa cibiyar, tare da kaddammar da ayyukan watsa labarai.
CMG zai yi amfani da fifikon da ya samu, na iya watsa labarai bisa hadewar fasahohin rediyo, da telabijijn, da sabbin kafofin watsa labaru, cikin harsuna 68, wajen watsa labarai dangane da ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka za su yi, da taron kungiyar APEC, cikin wani yanayi mai armashi, gami da gabatar da ra’ayi na kasar Sin don mutanen duniya su fahimta. (Bello Wang)