(Muna fara wa) da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.
Allah yana cewa a surar kausar
1. Hakika Mun ba ka alkausara. (Ruwan alkausara ko rabo ne mai yawa).
2. Saboda haka ka yi salla ga Ubangijinka. Ka kuma soke abar layyarka.
3. Hakika mai kinka shi ne, guntu (mai yankakken baya, mara alhairi).
Sallar Idi sunna ce mai karfi a kan ko wane namiji, baligi, da’ mai hankali, ba matafiyi ba. Kuma abar so ce bisa yara maza, da mace tsohuwar da ba a sha’awarta.
Yawan sallar Idi raka’a biyu ce. Babu bambanci tsakanin yadda a ke yin sallar Idin Karamar salla da ta Babbar Salla kuma ba ikama ba kiran salla se dai ajira liman kuma ba a nafila domin itama nafilace.
Ga yadda a ke yinta:
Tun farko mutum zai yi niyyar a zuciyarsa dan Annabi saw yace kuwani aiki yana tare da niyya, se ya yi niyyar koyi da liman ya ce, “ Na yi niyyar koyi da liman a cikin sallar Idi kaza” (ya fadi sunnanta ko Idin-Layya ko Idin-Ci). Daga nan liman zai ce ‘Allahu Akbar’ sau bakwai a cikin raka’a ta farko, tun kafin ya fara karatu (kabbarar haramar salla tana cikinsu). Shi kuma mai bin liman zai fadi ‘Allahu Akbar’ bayan fadar liman, har a cika kabbarorin nan bakwai. Amma sau daya kadai a ke daga hannu sama, watau a wurin kabbarar farko. Da kare fadar kabbarorin nan sai liman ya karanci Fatiha da sura a bayyane, amma am fi son surar Sabbih a cikin raka’a ta farko. Sa’an nan ya yi ruku’u da sujadai. Sa’an nan ya mike tsaye don yin raka’a ta biyu. Zai ce ‘Allahu Akbar’ sau shida kafin ya fara karatu (kabbarar mikewa tsaye tana cikinsu). Zai karanta Fatiha da sura a bayyane, amma am fi son surar Wasshamsi a cikin raka’a ta biyu. Sa’an nan ya yi ruku’u da sujadai, ya zauna, ya yi Attahiyyatu, sai ya sallame.
Bayan kake salla sai liman ya fuskanci Jama’a ya yi huduba biyu. Zai zauna a farkonsu da tsakaninsu. Zai fara ko wace huduba da kabbarorin, kuma ya yawaita fadarsu a hudubarsa. A lokacin nan ya ke fafa a cikin hudubarsa.
Yadda a ke gyraran Sallar Idi
Idan mutum ya sami liman yana tsakiyar karatu a cikin raka’a ta farko, ko ta biyu, sai ya yi niyya ya bi shi, ya fadi kabbarorin nan bakwai ko shida shi kadai. Idan kuwa ya sami liman ya rigaya ya yi wadansu kabbarori, sai ya bi shi ga sauran. Bayan liman ya cika nasa, shi kuma mai binsa sai ya kawo ragowar wadanda bai sami yi tare da liman ba.
Idan mutum ya tarad da liman yana ruku’u, sai ya yi niyya yasunkuya ga ruku’u ya same shi. Babu kome a kansa, salla tayi kyau.
Idan mutum ya sami raka’a ta biyu cikakiya tare da liman, idan zai rama ta farko, zai yi mata kabbarorin nan nata bakwai.
Idan liman ya kara wata kabbara a bisa adadin da aka iyakance, a kan mantuwa, mai koyi da shi ba zai fadi karin nan ba.
Idan liman ya rage kabbara daya ko abin da ya fi daya, bai tuna ba sai bayan ya yi ruku’u, to, zai yi sujada kabliyya. Idan kuwa gabannin ruku’u ne sai ya fadi kabbarar, kuma ya sake karatu daga farko. Zai yi ba’adiyya.
Idan mutum bai sami zuwa Masallacin Idi ba domin wani uzuri ko kuma da gangan, duk da haka an so ya yi sallan nan ta Idi shi kadai.
Mustahabban Idi
Mustahabbi ne mutum ya rayad da daren salla da yawaita ibada ga Ubangiji Allah. Kamar sallar nafiloli da karatun Alkur’ani da sauran addu’o’in da ya iya.
Kuma a ranar salla, abin so ne ga ko wane Musulmi, babba da yaro, mace da namiji, mai zuwa Masallacin Idi, da wanda ba ya zuwa, ya yi wanka salla. Am fi son mutum ya yi shi tun da asuba, watau bayan fitowar alfijir, kuma ana iya yinsa ko da rana ne idan mutum bai samu ya yi shi tun asuba ba.
Haka kuma abin so ne mutum ya sanya tufafinsa mafi kyau a ranar salla. Am fi son sababin tufafi in da hali. Haka kuma abin so ne mutum yabsan ya turare kuma abin so ne mutum ya tafi Masallacin Idi a kasa da kafafunsa. Amma a wurin dawowa gida bayan kare salla ya iya ya hau duk abin da ya ga dama. Kuma abin so ne mutum ya sake sabuwar hanya a lokacin dawowarsa daga Masallacin Idi.
Abin so ne ga wanda zai tafi Masallacin Idi ya yi ta yin kabbara tun daga fitarsa gida har isarsa masallaci. Kuma ya ci gaba da yin kabbaran nan har sa’ad da liman ya tashi fara salla.
Ga yadda mutum zai fada :
Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illallah, Allahu Akbar Allahu Akbar, Wa lillahil ham.
Idan mutum ba ya iya fadin dukan wannan, to, Idan ya yi ta maimaita ‘Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar ya isa.
Kuma ba laifi yara su yi ‘yan wasanni na farin ciki a ranar sallah.
Kuma abin so ne mutum ya ziyarci iyayi da sauran dangi dan ayi wa juna barka barka da juna, sai adinga kace wa Takabbalallahu Minna Wa Minkum.
BAYANI A KAN HUKUNCIN LAYYA
Yin layya sunna ce mai karfi a kan kowane musulmi wanda yake da ikon yinta, Ko wace shekara, da sharadin musulmin yazamo da ne ba bawa ba. Amma ba bambanci a kan zamowar musulmin nan babban baligi ko yaro, mace ko na miji. Wanda LAYYA ta kama shi ne mtum mawadaci, wanda ya mallaki kudin da zai sayi dabbar layya da su, kudin nan kuwa ba ya bukatarsu don wata lalura ta dole har shekarar badi. Kuma mutum zai yi layyan nan ga ko wane mutum wanda ciyar da shi ta wajaba a kansa. Ko ya hada niyar ladar layyarsa ga duk mutumin da ciyar dashi ta wajaba akansa.
Annabi S.A.W yayi LAYYA da rago biyu, ya yanka daya shi da mutanen gidansa gaba daya, da zai yanka na biyu kuma sai yace wannan kuma na fakirai ne wanda basu samu damar layyaba nayi musu daga yanzu har zuwa tashi alkiyama. Shiyasa idan layya tazo mutum yana bakin ciki baiyi ba sai a ce Annabi S.A.W ya riga yayi maka LAYYA. Wannan ya nuna kenan rago daya ya isa mutum dashi da iyalansa komai yawansu, idan kowa daga cikinsu bazai iyayi ba, wannnan kuma ya nuna ana iya siyan abun layya abawa iyaye ko malamai, ko talakawa, ko fakirai, kamar yadda Annabi S.A.W ya yankawa wasu ragon layya. kuma shi ya yanka su da hannunsa. Allah ya baka ikon bawa wasu ragunan LAYYA. Ameen.
DABBAR DA AKE LAYYA DA ITA .
Ana layya da tumaki ko awaki ko shanu ko rakuma. Wajibi ne a kula da shekarun dabbar. A cikin tumaki akalla sai wanda tayi wata takwas da haihuwa ce zata isa. A cikin awaki sai wanda yayi shekara guda har ya shiga ta biyu. A cikin shanu sai wanda ya shiga cikin shekara ta hudu. A cikin rakuma kuwa sai wanda ya shiga cikin shekara ta shida. A wajen LAYYA, rago ya fi daraja, sannan dandakakken rago, sannan tunkiya, sannan bunsuru, sannan dandakakken bunsuru, sannan akuya, sannan na saniya na miji ko rakumi na miji, sannan dandakakke, sannan saniya mace ko rakuma mace. A wajen hadaya kuwa akasin wannan tsari shi ne yafi daraja, ko da yake an gabatar da tumaki akan awaki. Bambanci tsakanin LAYYA da hadaya shi ne, A wajen LAYYA dadin nama akafi so, A wajen HADAYAH kuwa yawansa akafi so.
DABBAR DA BA TA LAYYA.
Dabba hudu bai halatta ayi layya dasu ba ko anyi kuwa LAYYA batayi ba. Wannan dabbobin su ne;
1. Dabba mai ido daya, ballai kuma makauniya wacce bata gani.
2. Dabba mara lafiya. Idan dabba tana da wata cuta babba ga jikinta, to bai halatta ayi layya da ita ba.
3. Dabba mai gurgunta. Idan dabba gurguwace har yan uwanta sukan tsere mata wajen tafiya, bai halatta ayi layya da ita ba.
4. Dabba kamaika. Wato marasa mai. Idan dabba bushashshiyace kuma ramammiya wanda bata da bargo a jikinta, bai halatta ayi layya da ita ba.
Banda wadannan aibobi guda hudu, duk sauran cutuka akwai hilafar maluma a cikinsu akan dabbar za ta ayi LAYYA ko ba za tayi ba. Ala kulli halin dai an so dabbar ta zamo mai lafiya sumul garau. Don haka ya kyautu a kiyaye ragowar aibobin nan da akayi hilafa a cikinsu, Su ne dabba mai tsagaggen kunne, ko yankakken kunne, ko yankakkiyar wutsiya (Bundi kenan), ko karyayyen kaho. Idan dayan wadannan aibobi ya zama kadan ne babu laifi anyi rangwame a gare shi.
RANAKUN YANKA DABBAR LAYYA.
Ana yanka dabbar LAYYA a ranar goma ga zulhajji, bayan hantsi na farko kuma idan liman ya yanka dabbarsa a masallacin idi. Wanda duk ya yanka kafin liman, to babu layyarsa. Ranakun da aka bayar dan yin layya uku ne. Wato ranar sallah da ranaku biyu masu binta. Wato ranar 10,11, da 12 ga zulhajj. Ana yanka dabba a kowace rana a cikin wannan ranaku guda uku ne kawai. Wato lokacin yan ka, shine, daga fitowar ranar har zuwa faduwarta duk lokacin yanka ne. Bai halatta ayi yanka acikin dare ba, idan kuwa anyi, to layya bata yi ba.
YADDA ZA A YI DA NAMAN LAYYA.
Abu uku a ke yi da naman layya, Sune mai layya ya ci, yayi sadaka, sannan yayi kyauta. Yin sadaka ga matalauta shine wajibi, ku ma ba a iyakance yawan abin da mutum zai bayar sadaka ba. Amma ci da yin kyauta sai idan ya ga dama. A wajen yin kyauta ana iya ba har kafiri idan a wuri daya ku ke zaune, ko kuwa ya ziyarce ku. Sai dai abin ki ne a aika masa da shi har gidansa. An rawaito cewa Annabi S.A.W da yayi LAYYA ansamu labarin sayyada Aisha ta rabar da naman. Sai ya ke tambayarta ina naman? Sai tace ai na rabar duka ya kare sai dai cinya kawai ya rage, sai Annabi yace ai duka sunanan sai dai wannan ne da zamu ci ya kare. Wannan yana nuna mana cewa indai ka rabar kana da lada da yawa. Wannan yana nuna mana cewa Aisha R.A ba marowaciya bace kuma wannan yana nuna mana kyakkyawar dabi’ar annabi don baiyi ta fada ba don tace ta rabar ba.
Bai halatta a siyar da naman LAYYA ba, Haka kuma bai halatta a siyar da fatarta ba bisa ga kauli mashhuri.
HADA KARFI
Bai halatta ba mutum biyu ko fiye da haka ba, su hada kudi su siya dabba don suyi LAYYA ba. Dalilin wannan hanin, domin an ce ita layya sunnah ce ga mai iko kawai. Amma ya halatta a yi tarayya ga lada. Kamar mutum daya ya sayi dabba da kudinsa shi kadai, sannan ya yanka ta domin kansa da kuma wadansu mutane daban. Ko kuwa wani mutum guda ya ba wadansu mutane dabba daya don suyi layya da ita. Wannan kam ya halatta. Tarayya ce a wajen kudi ko mulki kadai aka hana.
Ba a ba mahauci ladan aikin fida daga cikin naman layya. Zaka biya shi ladan fidarsa daban, sannan ka bashi nama sadaka ko kyauta idan ka ga dama.
Maganar da wadansu su kace, wai kafinka fara yiwa kanka layya sai ka fara da yi wa iyayenka dai idan matalauta ne, idan kuma mawadaci ne ya zama har ciyarda iyayenka ya wajaba a kanka, to, sun shiga cikin tsarin sauran iyalanka, kamar yayanka da matanka, wanda an so kayiwa kowannensu layya ko ka hadasu.
SIFFAR YANKA
Akwai abubuwan da suka wajaba ko suka zama mustahabbi game da yanka dabba ko tsuntsu.
1. Idan za a yanka dabbobi da dama, ana so kada a yanka daya a gaban idon wata
2. Anaso a ba dabbar ruwa ta sha kafin a yanka ta.
3. Ana so a wasa wuka tayi kaifi saboda kar yanka ya dauki lokaci mai tsawo. Ana so kuma kar a wasa wukar nan gaban idon dabbar.
4. Idan za a yankata, ana so a kada ita da sauki akan barin jikinta na hagu. Idan rakumi ne kuwa, anaso a soke shi daga tsaye bayan an dabaibaye shi.
5. Anaso a fuskantar da dabbar nan wajen alkibla
6. Wajibi ne mai yanka yayi niyyar yin yanka a cikin zuciyar sa. Wato niyar halatta cin naman nan. Idan mutum ya manta bai yi niya ba, ya halatta a ci naman nan.
7. Sannan bayan yayi niyya sai yace; BISMILLAH WALLAHU AKBAR, Sannan sai ya fara yanka. Fadar bismillah wajibi ne. Idan mutum ya manta da fadarta, ya halatta a ci naman. Karawa da fadar ALLAHU AKBAR mustahabbi ne, wato abin so ne. Haka kuma idan dabbar da za a yanka ta sadaka ce, kamar layya da suna da hadaya anaso a kara da fadan; RABBANA TAKABBAL MINNA, Wato UBANGIJINMU KA KARBAN MANA.
8. Sannan mai yanka ya saka wukarsa akan wuyan dabbar daga baya, ya yanke makogwaronta da wadansu jijiyoyi biyu na rabe da shi ta kowane gefensa. Ana kiran jijiyoyin nan JANNAYE. Idan mutum bai yanke dayan wannan abubuwa uku ba to yanka bai yi ba, ya baci. Haka kuma idan mutum ya fara yanka, ba zai dauke hannunsa ba sai ya gama yanka duka. Don haka idan mutum ya daga hannunsa bayan ya yanke sashen makogwaro ko jijiyar jannaye sannan kuma ya sake mayar da hannunsa ya karasa yanka to yanka ya baci, baza a ci ba. Amma an yafe laifin daga hannu dan lokaci kadan, kamar kubucewar wuka a tsakiyar yanka, ko wannan ma yana da hilafa don wadansu maluma sun ce baza a iya ci ba.
9. Bayan an gama yanka, anaso kada a fara fida ko figa sai bayan dabbar ta daina shure-shuren daukan ransu.
10. Wanda ya fara yanka daga keyar wuya, har ya kawo ga makogwaro da jijiyoyin jannaye biyu ya yanke su, yanka ya baci, baza a ci ba. Don dabbar ta riga ta mutu ta hanyar farawa da yanke lakar kashin wuyarta.
11. Wanda ya darzaza wuka ya yanke wuya baki daya har ya cire kai, za a ci naman ko da kuwa dagangan ne yayi haka sai dai yanke kai dagangan makruhi ne, wato abin ki.
12. Tumaki da awaki yankawa da wuka shine sunnar su. Rakumi kuma sokewa shine sunnarsa. Shanu kuwa da yankawa da sokewa duk daidai ne a garesu. Yadda ake soke dabba shine a saka wuka ko mashi a huda makogwaronta daga nan karshen wuya daga kasa. Dabbar da aka ce sunnarta yankawa ne, ko sokewa, idan an saba, ya halatta a ci naman.
13. Idan an yanka dabba mai ciki, yankar uwar ya wadatar da yankar dan.
14. Dabbar ruwa bata bukatar yanka ko da ta kan fito tudu ta shakata.
15. Idan mutum yana farauta ne, to, kafin ya harba kibiyarsa, ko bindigarsa, ko kafin ya jefa mashinsa ko sanda, ko kafin ya sake karensa, sai yayi niyyar yanka, ya kuma ce; BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, Idan ya samu makaminsa ya kashe wannan dabbar, sai a ci. Idan kuwa ya sameta da sauran rai, to, sai ya yanka ta.
16. kowane musulmi, mace ko na miji, yaro ko babba, yana iya yanka dabba. Amma an shardanta yaro ko yarinya su zama sunyi wayo, sun fahimci ma’anar yanka. A wajen layya anaso kowa ya yanka dabbarsa da hannunsa dan koyi da annabi.
Bai halatta a ci dabba mushe ba, wanda ba a samu an yankata ba harta mutu. Idan wani lahani ya samu dabbar har ta kusa mutuwa dominsa, idan lahaninnan yana daya da daga cikin wadannan abubuwa guda biyar;
1. Shakakkiya da igiya
2. Bugaggiya da sanda ko makamantansu
3. Wanda ta gangaro daga sama ta fado
4. Tunkurarriya da kaho
5. Wanda naman daji ya kama ya cinyeta.
To sai a duba a gani cewa, idan aka bar dabbar nan zata rayu? Idan aka barta in har zata iya rayuwa, to, ya halatta a yanka a ci. Idan kuma ko da an kyaleta bazata iya rayuwa ba, to ko an yanka bai kamata a ci ta ba. Ga alamomin da dabba bazata rayuwa ba idan sun sameta;
1.katsewar lakar kashin wuya dana baya
2. Yankewar jijiyar jannaye
3. Hujewar hanji
4. Cakudewar kayan ciki.
Idan ba dayan wannan aibobin guda hudu ne ya faru da dabba ba, to sai a yanakata a ci, koda kuwa ba a tsammanin zata rayu, bisa ga kauli mafi karfi.
Ya halatta ga mutum matsattse wanda yaji tsoron halakan ransa don yunwa, ya ci mushe. Kuma ya dauki guzuri har zuwa inda zai iya samun halattaccen abinci. An gabatar da cin mushe akan cin alade.
Ya halatta ayi amfani da fatar mushe ga kowane abu idan an jemeta, amma banda aikin ibada.
Fatar dabbobin da aka shardanta cinsu kamar giwa ko zaki da kura ko kyanwa, idan an yanka su, sannan kuma akayi musu tsarki ana iya yin sallah akan buzunta.
An shardanta yin amfani da hakoran giwa, a wani kauli kuma ya ce babu shardanci.
Farauta don sha’awa da wargi abin ki ne. Idan kuwa don neman abinci ne, to, ta halatta.
SP. Imam Ya Rubuto Daga Shalkwatar ‘Yansanda ta Zone 7 da ke Abuja