Duk da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya ke yi, kasar Sin ya tsallake kalubale da dama ta hanyar daukar mabanbantan ingantattun dabaru, tare da dora tattalin arzikin bisa tubali mai kwari domin cimma burinkanta na ci gaba na bana.
Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) sun nuna cewa, zuwa watan Oktoba, sayayyen kayayyakin masarufi, wanda shi ne babban ma’aunin karfin sayayya, ya karu da kaso 7.6 a kowacce shekara, wanda ya zama mafi sauri tun daga Mayu, haka kuma ya yi saurin karuwa daga kaso 5.5 da aka samu a watan Satumba.
- Ana Gudanar Da Dandalin FOCAC Game Da Raya Noma
- Yadda Ma’aikatan MDD A Nijeriya Suka Girmama Takwarorinsa Da Aka Kashe A Gaza
Masana’antar samar da kayayyaki ma ta zarce zaton kasuwa, inda ta samu karuwar kaso 4.6 a kowacce shekara a watan Oktoba. Wannan kuma shi ne ci gaba mafi karfi da aka samu tun daga watan Afrilu.
Bisa la’akari da manyan ma’aunan tattalin arziki, kakakin NBS Liu Aihua, ya ce tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da rike kuzarinsa na farfadowa a watan Oktoba, kuma ya shimfida tubali mai karfi ga kasar na cimma burikanta na ci gaba a bana. (Fa’iza Mustapha)