A ranar Laraba ne kotun daukaka kara ta tanadi hukunci kan karar da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya shigar na kalubalantar soke zabensa da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta yi.
In ba a manta ba, a kwanakin baya mun rahoto muku cewa, kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a wani hukunci da ta yanke a ranar 2 ga watan Oktoba, ta bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
- Farashin Kayayyaki Ya Karu Da Kashi 27.33 A Nijeriya – NBS
- Farashin Kayayyaki Ya Karu Da Kashi 27.33 A Nijeriya – NBS
Sule dai ya lashe zaben ne a karkashin jam’iyyar APC.
A zaman da aka yi a Abuja, jam’iyyun sun yi muhawara a gaban kwamitin mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Onyemenam Uchechukwu.
Bayan haka kwamitin ya tanadi hukuncin kuma ya ce za a sanar da ranar yanke hukuncin ga bangarorin biyu.