Abubuwan da za a bukata domin hadawa:
Kwano/mazubi biyu guda biyu, Kwai daya, Takarda/tissue, idan an tanadi wadannan, sai kuma a samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a tura fuskar.
Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan Kwai bayan an cire gwaiduwar, a kada farin ruwan Kwan har sai ya yi kumfa, daga nan sai a shafa ruwan Kwan a fuskar musamman ma kan kurajen,sai a yagi ’tissue’ kadan a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu, kada a yi magana sosai bayan an gama manna ’tissue’ domin yin hakan zai iya bude fuskar, wadda kuma ana sanya takarda din ne don ya matse fuska.
Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar, sannan sai a shafa gwaiduwar Kwan a fuskar na tsawon minti 15, sannan a wanke. A nan za a ga abin mamaki, a jarraba a ga banbanci.