Kungiyar kwallon akafa ta Manchester City ta dauki dan kwallon Leeds United, Kalvin Phillips kan kudi fam milayan 45 kuma dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 26, ya saka hannu kan yarjejeniyar kakar wasa shida da kungiyar da ta lashe Premier League a kakar da ta wuce.
Dan wasan ya zama na uku da Pep Guardiola’ ya dauka a bana, bayan Erling Haaland da kuma Stefan Ortega Moreno sai kuma Phillips, wanda ya buga wasanni 235 a kakar wasa takwas a Leeds United, yana da sauran kaka biyu kwantiraginsa ya karkare.
Phillips ya fara buga wa tawagar Ingila wasa a watan Satumbar shekara ta 2020, an kuma bayyana shi a matakin dan wasan Ingila da ya taka rawar gani a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021, wanda ya buga dukkan wasannin Euro 2020.
“Na zabi komawa kungiyar Manchester City ne domin buga wasa a karkashin mai koyarwa Pep Guardiola domin na san zan koyi abubuwa da dama a tare da shi saboda kasancewarsa daya daga cikin manyan masu koyarwa a duniya” in ji Phillips.
Philips dan wasa ne mai muhimmanci a karkashin koci, Marcelo Bielsa, ya yi wasanni 37 a Championship a kakar 2019 zuwa 2020, inda Leeds ta koma buga Premier League, bayan kaka 16 rabonta da gasar sai dai dan wasan ya sha jinya a kakar da aka kammala, amma ya buga wasa 20 a firimiya, sakamakon jinya da ya yi.