Hukumar ‘yansandan jihar Kano sun gargadi kungiyoyi da daidaikun jama’a game da kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Kano, kwamishinan ‘yansandan, Mohammed Usain Gumel, ya ce bayanan da aka samu sun nuna cewa, wasu mutane ne suka sha alwashin haifar da hargitsin siyasa a jihar.
- Yakin Zirin Gaza: An Kara Kwanaki Biyu Na Tsagaita Bude Wuta
- ‘Yansanda Sun Gargadi NNPP Da APC Kan Shiga Zanga-zanga A Kano
Ya ce rundunar ‘yansanda ba za ta kauce wa alhakin da ya rataya a wuyanta ba na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa a jihar.
Gumel ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba sannan kuma su yi kokarin kai rahoton duk wani yunkuri da kungiyoyi ko daidaikun mutane ke yi na haifar da hargitsi a jihar.
Akwai wasu mutane da ke fakewa da yin taron addu’o’in samun nasara a jihar domin tayar da hargitsi don cimma muradun siyasarsu.
Ya kara da cewa, akwai kuma wadanda ke ikirarin cewa suna cikin wasu kungiyoyin kasuwa ne da ke gudanar da zanga-zanga, su ma mun gano su kuma mun tarwatsa su.
Asalin ‘yan kasuwar na gaskiya sun nesanta kansu da masu zanga-zangar kuma sun bayyana goyon bayansu ga aikin ‘yansandan.