Kocin kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona, Xavi Hernandez ya bayyana cewar wasan da kungiyar za ta buga tsakaninta da Fc Porto a gasar Uefa Champions League na wannan satin zai zama tamkar wasan karshe.
Xavi ya bayyana cewar ya kamata kungiyar ta farfado daga abinda ya kira abin kunyar da tayi a wasansu na satin da ya gabata tsakaninsu da Rayo Vallecano a gasar Laliga ta kasar Sipaniya.
- Matashin Dan Kwallon Barcelona Guiu Mai Shekaru 17 Ya Jefa Kwallon Farko A Kungiyar
- Na Yi Mamakin Rashin Nasara A Hannun Arsenal -Xavi
“Dole ne mu dauki wannan wasan tamkar wasan karshe na Champions League domin shi kadai ne zai nuna idan zamu iya tabuka wani abin azo a gani a bana.
“Dole mu farfado daga abin kunyar da muka yi a gasar Laliga tsakaninmu da Rayo Vallecano” inji shi.