Kungiyar direbobin tanka masu dakon man fetur reshen Jihar Kaduna (PTD) da ke a karkashin kungiyar NUPENG, ta gargadi ‘ya’yan kungiyar da ke jihar da su yi watsi da duk wasu bayanan da suka fito daga wata majiya.
Kungiyar ta yi kashedin bin sanarwar uwar kungiyar ta kasa ta PTD, wadda sabon zababben shugabanta kwamarade Augustine Egbon da na sauran sabbin shugabaninta, suka fitar.
- Fintiri Ya Sanar Da Tallafin Dubu 10 Ga ‘Yan Bautar Ƙasa A Adamawa
- Kasurgumin Dan Daba, Hantar Daba Ya Mika Kansa Ga ‘Yansanda A Kano
Shugaban PTD na jihar, Abudullahi Haruna da aka sani da 63, ya yi wannan gargadin a taron manema labarai a Kaduna akan danbarwar rikicin shugabanci a kungiyar ta kasa.
A cewarsa, kungiyar ta PTD ta kasa da ke a karkashin NUPENG ta zabi sabbin shugabanninta na kasa, a ranar 31 ga watan Okutoba, 2023 a garin Ibadan na jihar Oyo, wanda shi ma ya zama daya daga cikin jagororin kungiyar ta kasa da ya fito daga Jihar kaduna.
Haruna ya ce, reshen na PTD na NUPENG, na da shiyya hudu ne da suka hada da Fatakwal, Kaduna, Warri da kuma Legas, inda sassa 172, suka yi zaben.
Haruna ya sanar da cewa, a rubuce yake cewa, tsohon mataimakin shugaban kungiyar na kasa Dayyabu Garga, ya rubuta wasikar sauka daga kan mukamin tun a 2022 biyo bayan zabarsa da aka yi a matsayin shugaban Karamar Hukumar Kanam ta Jihar Filato wanda kuma sakataren NUPENG na kasa, ya amince da wasikar sauka daga mukamin na Garga.