Hukumar lura da ayyukan kimiyya da fasahar sararin samaniya ta kasar Sin ko CASC, ta ce an kammala tsara aiki da hidimar tauraron dan Adam mai nisa irinsa na farko, wanda zai taimaka wajen samar da hidimar yanar gizo ko intanet mai matukar sauri.
CASC ta ce bayan harba wasu taurarin dan Adam na hidimar sadarwa, karfin yanar gizo daga tauraron dan Adam mai nisa daga doron duniyarmu, zai karade daukacin yankunan kasar Sin, da ma wasu yankuna na kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” ko BRI.
- Xi Ya Jaddada Bukatar Raya Tsarin Shari’a Mai Nasaba Da Ketare
- Jami’ar MDD: Sin Mai Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Tattalin Arzikin Zamani Na Duniya
Hidimar yanar gizon da za a samu daga wannan fasaha za ta kasance mai karfi sa sauri, inda za ta saukaka hidimomin sauke bidiyo, da gudanar da kira ta kafar bidiyo a intanet.
Ya zuwa karshen zangon bunkasa kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14, wanda ke gudana daga shekarar 2021 zuwa 2025, adadin karfin yanar gizo daga taurarin dan Adam masu nisa zai haura Gb 500 duk dakika.
Bayan kaiwa wannan mataki, karfin hidimar taurarin dan Adam na yanar gizo a kasar ta Sin zai bunkasa hidimomin sadarwa mai matukar sauri, da yanar gizo ga manyan fannoni da suka hada da sufurin jiragen sama, da hidimar taswira, da ayyukan gaggawa, da fannin makamashi, da kula da dazuka da tsirrai. (Saminu Alhassan)