Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, zai tafi birnin New York na Amurka domin jagorantar taron Kwamitin Sulhu na MDD kan rikicin Palasdinu da Isra’ila da za a yi a gobe Laraba.
Kasar Sin ta karbi ragamar shugabancin kwamitin sulhu na MDD a lokaci mai matukar muhimmanci da ido da hankalin duniya ya koma kan rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Palasdinu, wanda ya haifar da asarar rayuka da matsalolin jin kai.
- Sin Ta Kammala Tsara Aikin Tauraron Dan Adam Mai Nisa Na Farko Domin Samar Da Hidimar Intanet Mai Inganci
- Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu Sun Sake Karfafa Huldar Diflomasiyya
Duk da cewa lokaci ne mai muhimmanci, ina ganin duniya ta yi sa’a da samun kasar Sin a matsayin shugabar kwamitin a wannan lokaci, kasancewarta mai nuna halin dattako da sanin ya kamata. Na yi imanin cewa, bisa halinta da ma matsayin da ta dauka tun bayan fara rikicin na kin daukar wani bangare da kuma yadda ta shiga aka dama da ita, har da kada kuri’ar amincewa da kudurin tsagaita bude wuta a lokacin zama na gaggawa da MDD ta yi kan batun rikicin, kasar Sin za ta sauke nauyin dake wuyanta a matsayin babbar kasa.
Tun da dadewa, kasar Sin ta kasance mai neman warware rikicin na Palasdinu cikin lumana kuma bisa adalci ta yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa a yankin. Don haka, babu wata kasa da ta cancanci jagorantar batun warware rikicin kamar Sin. Kuma muna da Yakini a wannan karo yayin da take jagorantar kwamitin sulhu, za ta yi iyakar kokarin ganin an tabbatar da adalci kuma an lalubo bakin zaren.
Kamar yadda a kwanakin baya wakilan kasashen Larabawa da na musulmi suka kawo ziyara kasar Sin dangane da batun, saboda kwarin gwiwar da suke da shi kan kasar na karfin warware batun, na tabbata haka sauran al’ummomin duniya masu kaunar zaman lafiya ke da yakinin kasar Sin za ta iya yin kyakkywan tasiri wajen tabbatar da an tsagaita bude wuta da samun maslaha.
Duk da cewa, rikicin Palasdinu da Isra’ila ba abu ne da za a iya warware shi cikin wata guda na wa’adin kasar Sin ba, na tabbata, kamar a ko da yaushe, hangen nesa da sanin ya kamata da ma kaifin basirar kasar Sin za su kaita ga share fage ko saita alkiblar shawo kan rikicin da samar da hanyar zaman lafiya.