Yau Talata, kungiyar tuntuba da sada zumanta ta kasa da kasa ta kasar Sin da CMG sun yi hadin gwiwa don gabatar da dandalin sada zumunta na panda Basi na shekarar 2023 a birnin Dujiangyan na lardin Sichuan. Mataimakin shugaban kungiyar Cheng Guoping da mataimakiyar shugaban CMG Xing Bo sun halarci bikin.
Wannan dandali mai taken “Sada zumunta da more zaman lafiya”, yana da masu son sada zumunta kimanin 200 daga kasashen Amurka da Italiya da Belgium da Qatar da Morocco da Sri Lanka da sauransu. (Amina Xu)