Bahijja Malam Kabara, Shugabar Gidauniyar Amirul Jaishi, ‘yar jarida mai gwagwarmayar sauya tunanin mata a wannan karni, ta bayyana wa shafin Adon Gari bababn fatan da take da shi na sauya al’adar cudanya tsakanin mata da maza a wuraren bukukuwa. Ko ta yaya za ta cimma haka? Ga tattaunawarta da wakilinmu na Kano, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, kamar haka:
Za mu so ki gabatar wa da mai karatu kanki…
Sunana Bahijja Malam Nasiru Kabara, na yi karatun firamare a makarantarmu ta gida Ma’ahad Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara, daga nan na koma firamare ta Dawakin Kudu, sai kuma makarantar ‘yan mata ta ‘Yan Gaya, daga nan na samu sukunin halartar makarantar koyon shari’a‘School for Legal Studies’a Kano. Daga nan ne kuma, sai na fara aiki da ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kano. Bayan na fara aikin ne kuma na samu shiga budaddiyar jami’ar nan da aka fi sani ‘NOUN’, inda na yi karatun aikin jarida, aikin dana ke yi kenan har zuwa yanzu.
A bangaren karatun addini kuma kamar yadda aka sani, gidan maulana Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara; gidan ilimi ne, a nan na samu sukunin yin karatun addinina a bangare daban-daban, wadanda suka hada da ilmin Kur’ani wanda har musabaka a mataki daban-daban na yi, na karanta bangaren hadisi da fikhu da sauran fannonin ilimi, alhamdulillihi.
Tun da gidan Kabara na da alaka da kokarin tallafa wa harkokin ci gaban al’umma, shin ko ke ma na da irin wannan fata?
Wannan gaskiya ne, kuma dole na gode wa ‘ya’yan maulana Sheikh Muhammad Nasiru Kabara mata, wadanda duk shawarar da na ba su cikin gaggawa suke karba tare da ba ni goyon baya, wannan tasa na kirkiri Gidauniyar Amirul Jaishi, wadda muke mayar da hankali wajen tallafa wa mata da masu bukata ta musamman, sai kuma masu karamin karfi musamman Muhammadawa Kadirawa, ayyukan wannan gidauniya sun hada da bayar da tallafin karatu, koyar da sana’o’in dogaro da kai tare da shiga cikin harkokin samar da maslaha tare da kyautata mu’amalar zamantakewa.
Mene ne ya ja hankalinki wajen fara hangen tsaftace harkokin bukukuwa, musamman idan aka dubi batun cudanya tsakanin maza da mata a lokacin bukukuwa?
Alhamdu lillahi, duk wani mai kishin addini da kuma ganin yadda ake yi wa harkokin mutuntaka izgili, musamman yadda aka mayar da harkokin bukukuwa ta hanyar samun cudanya tsakanin mata da maza, wanda hakan wata babbar annoba ce, domin haduwar mata da maza annoba ce mai matukar ta da hankali da kuma yi wa harkokin addini karan tsaye, wanda ko shakka babu hakan ke jawo fushin Allah a daidai lokacin da ya kamata a yi masa godiya, yanzu an mayar da harkokin bukukuwa wurin cudanyar tsakanin maza da mata, wanda kuma Allah fushi yake yi da irin wadannan ayyuka.
Wane mataki kuke dauka don ganin kun kawo gyara a irin wannan hali da ake ciki?
Alhamdulillahi! Yanzu haka, na shiga shirin samarwa tare da horar da mata aikin DJ da daukar hoto da kuma MC, wadannan abubuwa su ne wadanda suka fi komai hadari a wuraren bukukuwa, za ka samu samari kadai ke yin kida a wuraran taron da mata ne zalla, mu kuma mata a duk inda muke da zarar mun ji kida shi kenan sai hankali ya koma can a rika rawa, wanda hakan ko kadan bai dace da tarbiyyar musulunci ba.
Wannan tasa zuwa yanzu na fara horar da mata aikin DJ, MC da kuma mai daukar hoto, wadanda idan taron mata ne su ne kadai za su gudanar da harkokin bikin tare da ‘yan’uwansu mata zalla, yanzu haka ni kaina na fara kokarin koyon aikin DJ, domin idan na iya shi kenan ni ma sai na shiga koyar da ‘yan uwana mata aikin na DJ, haka ita ma sana’ar daukar hoto da MC.
Wane kalubale kuke shirin fuskanta, musamman ganin ita wannan sana’a ta MC, DJ da daukar hoto, asalin masu ita za su kalli kamar kuna neman hanyar raba su da neman abincinsu?
Gakiya akwai babbar matsala, domin yanzu haka wanda duk na tunkara da nufin zai koya wa mata wannan sana’a ta DJ sai ya yi ta yi min yawo da hankali. Haka nan, su ma daga bangaren iyaye ina samun irin wannan kalubale, domin sai na gama magana da yarinya ta aminta da koyon aikin na DJ, kawai sai ka ji iyaye sun ce me zai sa mace ta kama sana’ar DJ, wallahi sai ka ga an sauya tunanin ‘yan matan. Amma alhamdulillahi, yanzu haka na samu gogaggaun makada Dj mata guda biyu, wadanda a halin yanzu sun iya komai, ni ma kuma yanzu zan fara koyon aikin na DJ, domin samun saukin koyawa sauran.
Mene ne fatan da kike da shi a kan wannan sabon tunani na tsaftace harkokin tarukan bukukuwa musamman a kasar Hausa?
Babban burina ko fatan da nake da shi shi ne, a wayi gari a ga duk wasu wuraren tarukan mata, ‘yan’uwansu mata ne ke yi musu kidan DJ, hoto da kuma MC. Sannan kuma, ina so maza su fahimci cewa; kowa da ka sani a wannan duniya iya rabonsa zai samu, yanzu haka akwai wasu gidajen manyan mutane a Kano da tuni sun karbi irin wannan shawara tawa kuma ni ce ke yi musu MC a wuraren bukukuwansu, hakan na kara farantawa Allah ganin an yi abin da Allah ke farin ciki ta fuskar kiyaye dokokinsa.
Wane abinci Malama Bahijja ta fi sha’awa?
Shayi ruwan bunu ko da madara, idan na sha shayi bukatata ta biya.
Wane irin sutura kika fi sh’awa?
Na fi sha’awar korayen tufafi.
Mene ne sakonki ga al’umma, musamman matan wannan zamani?
Sakona ba zai wuce na jawo hankalin mata a kan su ji tsoron Allah wajen dukkanin harkokinsu ba, haka su ma iyaye su yi kokarin yin kallon tsanaki ga tarbiyyar yaransu, domin amana ce Allah ya damka mana, sannan kuma wallahi ya yi alkawarin tambayar dukkanin abin da ya damka na manar tasa a gare mu. A karshe, ina fatan iyaye su ba mu hadin kai wajen barin yaransu, domin koyon wannan aiki da zai taimaka wajen tsaftace harkokin bukukuwanmu na yau da kullum.