Shugaban hukumar da ke gudanar da bincike kan ci gaban kimiyya da fasaha a sha’anin noma da masana’anu a Nijeriya, (NASENI), a takaice, Khalil Sulaiman Halilu, ya yi albishir wa al’ummar Nijeriya da cewa, nan da farkon shekara mai zuwa, hukumar za ta bijiro da wasu muhimman ayyukan da ta gudanar na bincike da kirkira da za su kawo saukin rayuwa ga al’umman kasar nan.
A cewarsa, hukumar ta dukufa wajen gudanar da muhimman binciken da za su kawo gagarumin sauyi da sauki wajen gudanar da harkokin rayuwa ta hanyar rungumar kimiyya da fasaha hadi da kire-kire na zamani.
- Sama Da Kamfanoni 5,600 Ne Suka Shiga Baje Kolin Sassan Motoci Na Shanghai
- Basirar Henry Kissinger Abu Mai Daraja Ne Ga Amurka
Halilu ya ce, hukumar ta jima tana gudanar da bincike kan kimiyya da fasaha a bangarori daban-daban kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu domin suna fitar da abubuwa da dama da suka kera domin kyautata rayuwa.
Ya yi karin haske kan hukumar NASENI da cewa, hukuma ce da take gudanar da bincike da kirkirar abubuwan da za su kawo wa jama’a saukin rayuwa musamman na zamani kamar su harkokin kwamfuta (na’ura mai kwakwalwa), harkokin da suka shafi masana’antu da kuma harkokin da suka shafi ci gaba na kiwon lafiya da sauran bangarori.
Inda ya ce, suna gudanar da bincike domin su gano matsalolin da ake tattare da su a cikin al’umma tare da kirkiro abubuwan da za su kawo sauki, bugu da kari su kuma koyar da sauran masana’antu yadda za a yi amfani da sabbin abubuwan da aka gano domin samar da rayuwa mai sauki a cikin al’umma.
A cewarsa, a baya-bayan nan hukumar tana kera farantan wuta da ke amfani da hasken wutar rana a jihar Nasarawa kuma jama’an kasa daga sassa daban-daban na saya domin amfani da shi.
“Kuma akwai solar home system na’ura ce da ta ke bayar da hasken wuta a gida ta hanyar farantan wuta mai amfani da hasken rana da jama’a musamman a yankunan karkara ke saya domin amfanuwa.”
“A bangaren noma akwai taki na musamman da muka kirkira shi ma muna kan ganin yadda za mu samar wa manoma. Idan ka duba harkar kwamfuta akwai irin su manhajoji (softwares) kala-kala da muka yi suna ma na kawo sauki wajen gudanar da harkokin kasuwanci.”
Shugaban ya kara da cewa, a bangaren kiwon lafiya kuwa, sun kirkiro abubuwa da dama kamar su rigakafi nau’ika daban-daban dukka domin kawo wa jama’an Nijeriya saukin rayuwa.
“Muna son kafin karshen wata hudu na shekarar 2024 mutanen Nijeriya za su fara ganin irin ayyukanmu daban-daban.
“Akwai abun da ake kira technology transfer, ka ga wani kirkira a wata kasa ya maka kuma kana son ka kawo kasar ka. A Nijeriya hukumarmu ce take karban irin wannan kirkire-kirkiren da aka yi a wasu kasashe domin mu kawo su cikin gida Nijeriya tare da gyarashi zuwa irin yanayinmu da al’adunmu.
“Saboda haka mun kulla yarjejeniya da China wanda za su kawo kudi kimanin dala biliyan shida wanda za a yi amfani da shi wurin debo irin abubuwan da suka yi wanda muke da sha’awarsu a kai domin mu kawo cikin kasarmu domin taimaka wa al’umman Nijeriya,” a cewar Khalil Sulaiman.
Daga bisani ya yi kira ga matasa masu kaifin basira da suke kirkire-kirkiren abubuwa musamman a bangaren kimiyya da fasaha da zo domin hada kai da hukumar NASENI domin yin aiki mai nagarta wajen samar da saukin rayuwa musamman a bangaren bunkasa tattalin arziki da taimakon juna.