A kwanan baya, yayin da yake hira da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, babban edita na kafar watsa labarai ta “Ghana Web”, Roger Agana, ya yi tsokaci kan taron koli na kafofin watsa labaru na duniya karo na 5, dake gudana a kasar ta Sin. Inda ya ce taron ya hallara kafofin watsa labaru fiye da 10 na kasashen Afirka, wadanda ya kamata su yi kokarin bayyana yadda Afirka da Sin suke hadin gwiwa da juna, bisa dandalin da aka ba su.
A cewarsa, taron nan wata dama ce mai kyau ga kafofin watsa labaru na Afirka, don su musanya ra’ayi da takwarorinsu na sauran kasashe, ta yadda za a iya karfafa fahimtar juna da hadin kai, don tabbatar da makomarsu mai haske.
- Xi Jinping Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Kasa Da Kasa Na Congdu Na 2023
- Shugaba Xi Ya Yi Kira Da A Ingiza Muhimmiyar Rawa Da Tsarin Mulkin Kasa Ke Takawa A Fannin Jagorancin Kasa
Ban da haka, jami’in na kasar Ghana ya ce, ana son ganin ainihin abubuwan da suke faruwa a kasashen Afirka da kasar Sin, da yadda bangarorin 2 ke karfafa hadin gwiwarsu, wadda ke haifar da alfanu ga al’ummunsu. A cewarsa, hadin kan Afirka da Sin abin koyi ne ga sauran kasashe, saboda haka yana da yakini kan cewa, duk wata kafar watsa labaru dake nahiyar Afirka tana da dimbin abubuwa masu alaka da hakan da take son gaya ma mutanen duniya.
A cewar jami’in, a cikin shekaru 10 da suka gabata, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar ta sa aka samu karin layukan dogo, da tashoshin jiragen ruwa, da na saukar jiragen sama a nahiyar Afirka, ta yadda aka inganta kayayyakin more rayuwa a nahiyar, da samar da ci gaban tattalin arziki, gami da hakikanin alfanu ga jama’ar kasashen Afirka. (Bello Wang)