A jiya Lahadi, an kawo karshen taron kasa da kasa mai taken “Fahimtar kasar Sin” na shekarar 2023, a birnin Guangzhou dake kudancin kasar, wanda ya samu manyan kusoshi fiye da 600 da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 30 masu halartar taron.
A wajen taron na wannan karo, baki na kasar Sin da na kasashen waje sun yi bayani kan yadda kasar Sin take zamanintar da kai, da tasirinsa mai yakini kan kasashe daban daban. A ganinsu, ta hanyar gudanar da taron, an samu damar rage bahaguwar fahimtar da ake samu tsakanin mabambantan kasashe da al’adu, da taimakawa samun fahimtar juna tsakanin al’ummun Sin da na sauran kasashe.
- Babban Edita Dan Kasar Ghana: A Bayyana Yadda Sin Da Afirka Suke Hadin Gwiwa Da Juna
- Kasar Argentina Ta Ba Shugaban CMG Lambar Yabo
Cikin bakin da suka bayyana ra’ayoyinsu a wajen taron, Ashok Kantha, tsohon jakadan kasar Indiya a kasar Sin, ya ce kasar Sin kasa ce wadda karfin tattalin arzikinta ya kai matsayi na biyu a duniya, wadda ta samar da dimibin gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Kana da kasar Indiya da kasar Sin dukkansu sun amfana bisa tsari na dunkulewar tattalin arzikin duinya.
A nasa bangare, Mushahid Hussain Sayed, shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa ta kasar Pakistan, ya ce shawarwarin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, masu alaka da ci gaban tattalin arziki, da tabbatar da tsaro, da kare al’adu da wayewar kai a duniya, sun sa ana iya kallon kasashe daban daban a matsayin wata hadaddiyar al’umma, maimakon mai da hankali kan moriyar wata kasa ita kadai.
Ban da haka, Huang Renwei, mataimakin shugaban cibiyar nazarin manyan tsare-tsaren da suka shafi kirkirar sabbin fasahohi da ci gaban harkoki ta kasar Sin, ya ce, akwai dimbin fannonin da ake iya samun moriyar bai daya tsakanin kasashen Sin da Amurka, saboda haka ya kamata kasashen 2 su yi kokarin habaka moriyarsu ta bai daya, da magance samun sabanin ra’ayi. (Bello Wang)