Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya yi jawabi karkashin ajandar babban taron MDD karo na 78, bisa taken “Karfafa hadin gwiwar taimakon jin kai da rage radadin bala’o’i na MDD”, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa hadin kai da hadin gwiwa, da yin aiki tare don taimakawa kasashen da ke fama da matsalar jin kai su shawo kan matsaloli da kalubale.
Dai Bing ya ce, kimanin mutane miliyan 364 a fadin duniya ne ke bukatar agajin jin kai, kuma yawan kudin da ake bukata don ba da agajin jin kai ta kai dalar Amurka biliyan 55.9, amma masu ba da agaji sun ba da dalar Amurka biliyan 18.3 kawai, wanda ya kai kashi 32.7 bisa 100 na adadin abin da ake bukata. Kasashen da suka ci gaba, a matsayinsu na manyan masu bayar da agajin jin kai, wadanda ke da alhakin tarihi, ya kamata su cika alkawurran da suka yi wajen bayar da gudummawar a kan lokaci da cika alkawurran bayar da agajin da kuma cike gibin tallafin jin kai yadda ya kamata.
- Tsohon Firaministan Austria: Ra’ayin “Raba Gari Ta Fannin Tattalin Arziki” Bai Dace Ba
- Yadda Kasar Sin Ke Ba Da Gudummawar Tinkarar Sauyin Yanayi A Duniya
Dai Bing ya kara da cewa, tun bayan barkewar rikicin Palasdinawa na Isra’ila, a halin yanzu al’ummar Palasdinawa musamman mata da kananan yara a yankin zirin Gaza, na fuskantar hasarar rayuka baya ga raba su da muhallansu. Yanayin zamantakewa da tattalin arziki ya ruguje, kana abubuwan more rayuwa sun lalace matuka. Mutane fiye da miliyan 2 a zirin Gaza na cikin mawuyacin hali. Don haka ya kamata al’ummomin kasa da kasa, su inganta tsagaita bude wuta mai dorewa da daukar managartan matakai don kare rayukan fararen hula, musamman mata da kananan yara, da hanzarta dawo da ayyukan jin kai.
Ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance mai kiyaye zaman lafiya a duniya, kuma mai sa kaimi ga samun ci gaba tare, da himmantuwa wajen inganta aikin gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. (Ibrahim)