Hukumomi sun tabbatar da mutuwar wata ma’aikaciyar jinya da ‘yarta, sakamakon hatsarin jirgin ruwa a garin Gamadio da ke karamar hukumar Numan a Jihar Adamawa.
Shugaban karamar hukumar Numan, Honarabul Christopher Sofore, ya bayyana haka ga tawagar gwamnatin jihar da mataimakiyar gwamna Farfesa, Kaletapwa George Farauta, ta jagoranta, zuwa garin a ranar Litinin.
- “Isra’ila Ta Kama Yara 245, Mata 147, ‘Yan Jarida 41 Da Wasu 1,666 Bayan Tsagaita Wuta”
- MDD Za Ta Sake Shirya Taron Kada Kuri’a Kan Tsagaita Wuta A Gaza
Ya ci gaba da cewa “mutum biyar ke cikin jirgin ruwan lokacin da hatsarin ya faru, an yi nasarar kubutar da mutum uku, amma mutum biyu, jami’an NEMA sun tabbatar da mutuwarsu” inji Sofore.
Da ta ke maida martani,vmataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta kalubalanci hukumomin bada agajin da su tilasta amfani da rigar-Kariya (life jacket), da cewa zai takaita rasa rayuka da dukiyoyin ake Koda hadarin ya auku.
Ta ci gaba da cewa “dole mu dauki matakan kare rayukan jama’a, shugabannin kananan hukumomi, su tabbatar Rigar-Kariya (life jacket), ta wadata a yankunan kananan hukumomin da ake samun matsalar hatsarin ruwa” in ji Farauta.
Mataimakiyar gwamnan ta kuma jajanta wa iyalai da jama’ar yankin Gamadio, game da rashin, ta kuma karfafa batun amfani da Rigar kariya duk lokacin da jama’a za su shiga jirgin ruwa.