Mataimakin daraktan sashen tsare-tsare na ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin Wu Jiaxi ya bayyana cewa, ya zuwa karshen watan Nuwamba, yawan yankunan raya fasahar zamani ya kai 178.
Wu Jiaxi ya bayyana cewa, a watanni tara na farko na wannan shekarar da muke ciki, yawan karuwar tattalin arzikin wadannan yankunan raya fasahar zamani, ya kai kudin Sin RMB yuan triliyan 12.33, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.73, wanda ya karu da kashi 7.11 cikin 100 kan na makamancin lokaci na shekarar da ta gabata.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp