Wakilin Hukumar Samar da Abinci ta duniya (WFP) ta MDD a jamhuriyar Congo Mamadou Mbaye, ya bayyana a ranar 11 ga wata cewa, gwamnatin kasar Sin ta ba da gudummawa sosai wajen tabbatar da wadatar abinci a kasashen Afirka da ma duniya baki daya, ta hanyar ba da tallafin abinci ga kasashen Afirka.
A wannan rana, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Congo Li Yan da Mbaye sun rattaba hannu kan takardar shaidar kammala aikin ba da agajin abinci na gwamnatin kasar Sin tare. Da yake zantawa da manema labarai bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, Mbaye ya ce, a duk lokacin da kasashen Afirka ke fuskantar matsaloli, kasar Sin tana ba da taimako a kan lokaci. Kasar Sin ta gudanar da ayyuka da dama na hadin gwiwa tare da hukumomin MDD a nahiyar Afirka, inda ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen tabbatar da wadatar abinci a kasashen Afirka ciki har da Jamhuriyar Congo, wanda jama’ar Afirka suka yi maraba da su tare da nuna godiya sosai.
A watan Yulin shekarar 2021, gwamnatin kasar Sin ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ba da agajin abinci da Hukumar Samar da Abinci ta duniya (WFP) don taimakawa jama’ar Jamhuriyar Congo da annobar COVID-19 ta shafa. An yi nasarar aiwatar da aikin a watan Agustan shekarar 2023, wanda ya amfanar da jimillar mutane kusan 168,000. (Muhammed Yahaya)