A shekarun baya bayan nan, musamman a lokacin da ake fama da tafiyar hawainiya a fannin raya tattalin arzikin duniya, karin kasashe masu tasowa, ciki har da na nahiyar Afirka, suna mayar da hankali ga muhimmancin raya fannin tattalin arziki na dijital, wato sassan tattalin arziki da ake rayawa ta amfani da fasahohin sadarwa.
A kasar Sin wannan fanni ne da ya samu matukar ci gaba, wanda kuma a baya bayan nan kasar ta karkashin kamfanonin ta masu kwarewar fasahohi, ke shigar da fasahohinsu na dijital cikin sassan kasashen nahiyar Afirka, ta yadda nahiyar ke samun karin dunkulewa da juna, da ma sauran sassan duniya. A hannu guda kuma, kasashen nahiyar sun fara cin gajiya daga tarin alfanun dake tattare da dabarun raya wannan fanni na tattalin arziki.
- Xi Ya Yi Musayar Sakon Taya Murna Da Takwaransa Na Kenya Kan Cika Shekaru 60 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Kenya
- Sin Ta Gudanar Da Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Halaka A Birnin Nanjing
Sanin kowa ne cewa, gina fannin tattalin arziki na dijital, hanya ce ta cimma moriya mai tarin yawa a kasuwanni da cibiyoyin hada-hadar kudi, kuma kasashe masu tasowa ciki har da na Afirka, na da ikon samun kaso mai tsoka daga dunkulewar duniya waje guda da fannin ke haifarwa.
Kamar dai kasar Sin, su ma kasashen Afirka na da babbar kasuwa ta cinikayyar hajoji, da matasa dake cikin lokutan kwadago, don haka dabarun kasar Sin na raya tattalin arziki na zamani, a fannin hada-hadar kudade, da inshora, da sayayyar kayayyakin bukata na yau da kullum, da dunkule sassan kasuwanni, za su ci gaba da amfanar kasashen Afirka yadda ya kamata.
Sai dai duk da tarin alfanun wannan fanni, kasashen Afirka na da babban gibi, kafin su kai ga matsayin cin gajiyar tattalin arziki na dijital yadda ya kamata, sakamakon karancin manyan ababen more rayuwa, da karancin kwarewa ta ilimin da ake bukata domin sarrafa naurori masu nasaba.
Masharhanta na ganin idan har nahiyar Afirka ta kai ga shawo kan wadannan matsaloli, to hakan zai ba ta damar cike gibi, da ratar da sauran sassan duniya masu ci gaba suka ba ta. Kuma albarkacin shigar kamfanonin fasahohin sadarwa na Sin irin su Huawei, da sauransu, wadanda ke samar da manyan fasahohin sadarwa, kamar manyan turakun yanar gizo, da sauran fasahohi masu nasaba, sannu a hankali Afirka za ta kai ga cimma nasarorin da ake fata.
Don haka babban buri a nan shi ne, dorewar hulda mai kyau tsakanin Sin da kasashen Afirka, a fannonin wanzar da ci gaba, ciki har da wannan muhimmin fanni na raya tattalin arziki na dijital, wato wanda ake gudanarwa ta amfani da naurorin zamani.(Saminu Alhassan)