Ministan kasafin kudi da tsara tattalin arizikin kasa, Atiku Bagudu ya bayyana cewa, naira biliyan 100 da gwamnatin tarayya ta ware a cikin kasafin kudin shekarar 2024, zai taimaka wajen baiwa fannoni masu zaman kansu damar zuba jari a harkar noma a wannan kasa.
Bagudu ya bayyana hakan ne, a yayin da ya bayyana a gaban kwamatin da ke kula tare da bibiyar kashe kudin wannan ma’aikata ta noma a majalisar wakilai.
Sannan ya kara da cewa, wannan kudi da aka ware wa wannan ma’aikata, yana cikin shirin bayar da rance wanda zai taimaka wa fannin na aikin noma.
- Manoman Karkara Sun Nuna Farin Ciki Da Yadda Suka Amfana Da Tallafin IFAD
- Kasashe 5 Da Nijeriya Ta Fi Shigo Da Kayayyakinsu
“Wannan kasafi, ba wai ya kunshi komai da komai ba ne na kudaden da za a kashe, duk da dai cewa an dauki matakai domin samo kudade daga wasu hanyoyi daban-daban.
A cewar tasa, tuni aka rattaba hannun yarjejeniya da kamfanin Siemens na Kasar Jamus, wanda zai taimaka wa Nijeriya a fannin samar da wutar lantarki.”
Sannan Ministan ya bayyana cewa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kafa wani kwamiti da zai samar da kudade daga wajen kasafin wannan kudi.
Haka zalika ya kuma bayyana cewa, akwai abubuwa da dama wanda masu zuba hannun jari za su iya yi.
“A matsayina na Minister, zan yi kokarin gayyato masu zuba hannun jari, don su zuba jarinsu a wannan fanni na aikin noma a wannan kasa,” in ji shi.