Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf ya rasu yana da shekaru 86, an nada Sheikh Meshaal a magajinsa bayan shafe shekaru uku yana mulki a kasar.
Hukumomin kasar dai ba su bayar da wani musabbabin mutuwar tasa ba, amma sun sanar da fara zaman makoki na kwanaki 40 a hukumance da kuma rufe ma’aikatun gwamnati na kwanaki uku.
An kuma nada Yarima mai jiran gado na Kuwait din dan uwan shi, Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, a matsayin sabon sarki, in ji Issa Al-Kandari, mataimakin firaminista kuma karamin ministan harkokin majalisar ministocin kasar.
An rantsar da Sheikh Nawaf ne a watan Satumbar 2020 bayan rasuwar dan uwansa, Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, a Amurka yana da shekaru 91.