• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin Na Musamman Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Madagascar

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Madagascar Andry Nirina Rajoelina ya yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Hu Chunhua, ya halarci bikin rantsar da shugaba Rajoelina da aka yi ranar Asabar, ya kuma gana da shi a jiya Lahadi.

Hu ya mikawa Rajoelina sakon gaisuwa da fatan alheri daga Xi. Ya ce kasar Sin tana mai da hankali matuka kan raya dangantakar dake tsakaninta da Madagascar, kuma tana son yin aiki tare da Madagascar, don zurfafa mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, da ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan muhimman batutuwan dake shafar moriyarsu, da ciyar da hadin gwiwarsu zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare kuwa, shugaba Rajoelina ya gode wa shugaban kasar Sin bisa aiko da manzo na musamman don halartar bikin rantsar da shi, inda ya bukaci Hu da ya mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga Xi.

Ya bayyana cewa, Madagascar tana mutunta dadadden zumuncin dake tsakaninta da Sin, kuma a shirye take ta kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a muhimman fannoni kamar aikin gona, da masana’antu, da makamashi da albarkatun jama’a, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani babban matsayi. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Daga Birnin Sin

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Next Post
Xi Ya Saurari Rahoto Daga Manyan Jami’an Gwamnatocin HK Da Macao

Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025
Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

October 31, 2025
Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

October 31, 2025
Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.