A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da jagoran gwamnatin yankin musamman na HK John Lee a birnin Beijing, lokacin da John din ke ziyarar aiki a Beijing. Yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya saurari rahoton halin da yankin HK ke ciki daga mista Lee, da ma ayyukan gwamnatin yankin.
Da yake tsokaci yayin tattaunawar, Xi ya ce cikin tsawon shekara guda, karkashin jagorancin babban jami’i John Lee, gwamnatin yankin musamman na HK ta yi rawar gani, wajen sauke nauyin dake wuyan ta tare da cimma manyan nasarori, kana ta tsaya tsayin daka wajen kare tsaron kasa, da kyautata salon gudanar da majalissun yankin, da cimma nasarar kammala zaben ‘yan majalissun yankin, kana ta tsame yankin HK daga mawuyacin halin fama da annoba, tare da tabbatar da farfadowa daga dukkanin fannoni.
- Sin Ta Zartas Da Dokar Sanya Ido Da Jagorancin Cibiyoyin Hada-hadar Biyan Kudade Da Ba Na Banki Ba
- Gwamnatin Kano Za Ta Binciki Musabbabin Gobarar Da Ta Tashi A Karamar Hukumar Gwale
A daya bangaren kuma, shugaba Xi Jinping ya gana da jagoran gwamnatin yankin musamman na Macao Ho Iat Seng, wanda shi ma ke ziyarar aiki a birnin Beijing. Yayin da suke tattaunawa a Litinin din nan, Xi ya saurari rahoto daga Ho, game da yanayin da yankin Macao ke ciki, da ayyukan gwamnatin yankin.
Shugaba Xi ya ce a tsawon shekara guda, jagoran gwamnatin yankin musamman na Macao Ho Iat Seng, ya jagoranci yankin bisa gaskiya, tare da sauke hakkin shugabanci bisa tsari, kana ya cimma nasarar kammala bitar dokar Macao ta tabbatar da tsaron kasa, ya kuma gudanar da aikin sake nazarin dokar zaben shugaban yankin, da ta zaben ‘yan majalissar dokoki bisa tsari. Kaza lika ya samar da cikakken tsarin bunkasa ci gaban Macao mafi inganci a tarihi, wanda hakan ya sanya tattalin arzikin Macao ya farfado cikin sauri, kuma yanayin zamantakewar yankin ya ci gaba da gudana bisa daidaito da lumana. (Mai fassara: Saminu Alhassan)