A ranar Talata Malaman addinin Musulunci a birnin Kano sun gudanar da addu’o’i na musamman don ganin dan takarar gwamna na jam’iyyar (APC), Dr. Nasiru Gawuna, ya samu nasarar zama gwamnan Kano a hukuncin da kotun koli ake sa ran za ta yanke.
Malaman da suka fito daga manyan Kungiyoyin addinin Musulunci uku, sun yi addu’a ga alkalan kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano da na kotun daukaka kara da ke Abuja bisa abin da suka kira watsi da shari’a da aka shigar ana kalubalantar jam’iyyar APC reshen jihar kan takaddamar kujarar gwamnan jihar.
- Kotu Ta Kori Karar Abba K. Yusuf Ta Tabbatar Da Hukuncin Kotun Zabe Da Ya Tabbatar Da Gawuna
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
Idan za a iya tunawa dai kotun sauraron kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun bayyana Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Kungiyar Malaman da suka hada da Tijjaniyya da Izala da Kadiriyya sun gabatar da addu’o’in ga Alkalan Kotun Koli da Kotun Daukaka Kara da mayarwa mutanen Kano hakkinsu na abun da suka zaba.
Malaman sun samu wakilci da suka hada da Sheikh Albakry Mikail daga Darikar Tijjaniyya da Malam Garba Yusuf Abubakar na kungiyar Izala da Farfesa Maibushira daga darikar Kadiriyya sun bukaci kotun koli da ta duba hujjojin da ke gabanta ta kuma tabbatar da Gawuna a matsayin halastaccen gwamnan Kano.
A cewar Malam Abubakar, an gudanar da addu’o’in ne domin tabbatar da adalci da galaba a kan magoya bayan jam’iyyar NNPP a Kano.
Ya ce: “Mun taru a nan ne domin yin addu’o’i ta musamman ga alkalan kotun koli da kira ga alkalan kotun koli da su yi duba da kyau da hujjojin da ke gabanta, su kuma yi wa al’ummar Jihar Kano adalci don kwato musu nasararsu da aka sace.”