Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Pupule na yankin karamar hukumar Yorro ta jihar Taraba, inda suka sace mutum 23 ciki har da basarake mai daraja ta biyu da fadawansa.
BBC ta rawaito cewa, lamarin ya afku ne a ranar Talata da daddare inda ‘yan bindigar masu yawan gaske suka shiga garin tare da kewaye shi.
- An Sace Mai Ciki, Hakimi Da ‘Yansanda A Taraba
- Mutane 32 Sun Mutu A Wani Sabon Hatsarin Kwale-kwale A Jihar Taraba
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa, ba su san adadin ‘yan bindigar da suka shiga garin nasu ba saboda yawansu.
Ya ce,” sun shiga cikin dare suka dauki na dauka suka bar na bari, kuma a cikin wadanda suka dauka baya ga basaraken da dogarinsa, akwai limamin masallacin Jumma’a da fastoci biyu da kuma sauran jama’ar gari.”
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun fasa shaguna tare da satar kayan abinci da abubuwan sha.
“Ba wannan ne zuwan su na farko ba, wannan shi ne karo na hudu da suka je garinmu” In ji mazaunin garin na Pupule.
Tuni dai rundunar ‘yan sanda Nijeriya reshen jihar ta Taraba ta ce ta fara bincike tare da neman mutanen da aka sacen.
Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Usman Jada, ya ce suna samun labarin abin da ya farun, nan da nan kwamishinan ‘yan sandan jihar bai yi kasa a gwiwa ba ya tura wani sashe na musamman na jami’ansu wadanda ke kula da masu satar mutane domin su je garin da kuma bin sawun ‘yan bindigar.
Ya ce an baza jami’an tsaro a jejin domin neman mutanen da aka sace, “amma har yanzu ba mu ji komai ba,” a cewarsa.
Jama’ar garin na Pupule dai, sun ce a duk hare-haren da aka kai masu sau uku a can baya, wannan shi ne mafi muni da tayar da hankali, kuma sun yi kira da a girke masu karin jami’an tsaro a yankin.
Matsalar tsaro a Najeriya dai na ci gaba da zama ruwan dare gama duniya musamman ta masu satar mutane domin kudin fansa a yankunan arewa maso yammacin kasar da kuma wasu yankuna na arewa maso gabashin kasar.
Kuma duk da kokarin da gwamnatin tarayyar kasar ta ce tana yi don kawo karshen wannan matsala har yanzu ba ta sauya zani ba.