An gudanar da taron koli na shekara shekara na kasar Sin, game da ayyukan raya yankunan karkara, a ranaikun Talata da Laraba a nan birnin Beijing, inda aka fayyace muhimman ayyukan raya karkara da za a gudanar a shekarar 2024 dake tafe.
Yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin umarni, game da ayyukan da suka shafi noma, da inganta yankunan karkara da rayuwar manoma.
Shugaba Xi ya ce a shekarar nan ta 2023, an shawo kan tarin kalubale, ciki har da na tasirin bala’u daban daban. A daya bangaren kuma, an samu yabanyar hatsi mafi yawa a tarihin kasar, kuma kudaden shigar manoman kasar ya karu sosai, yayin da rayuwar mazauna karkara ke kara inganta da daidaita.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kaucewa Aiwatar Da Matakan Da Ka Iya Barazana Ga Tsaronta
- Sin Na Matukar Adawa Da Sukar Da Amurka Ke Yiwa Dokar Tsaron Kasa Ta HK Da Batun Sayarwa Taiwan Makamai
Ya ce domin ingiza salon zamanantarwa na Sin, dole ne a yi aiki tukuru, wajen karfafa tushen noma, da farfado da yankunan karkara a dukkanin fannoni. Xi ya ce bisa kwarewar da Sin ta samu karkashin manufar farfado da kauyuka ba tare da gurbata muhalli ba, dole ne a kara himma wajen aiwatar da takamaiman manufofi bisa yanayin da ake ciki, a kuma yi aiki sannu-sannu, daki-daki wajen wanzar da nasarori, har a kai ga cimma sakamako na zahiri da zai amfani al’umma.
Har ila yau, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin tabbatar da samar da isasshen abinci, ta hanyar daidaita adadin filayen noma da ake bukata domin noma hatsi, da fadada yabanyar da ake girbewa a fadin gonakin. Kana a yi aiki wajen kafa tsarin samar da abinci ta fannoni da dama, tare da kara inganta yanayin kasar noma.
Ya ce domin ingiza sauri da harsashi a tsarin zamanantar da noma, ya kamata a karfafa matakan kimiyya da fasahohi, da fannonin kwaskwarima, a kuma kara azama wajen cimma nasarar cin gajiya daga fasahohi, tare da kara inganta tsarin ayyukan gona, da habaka yankunan karkara da rayuwar manoma. (Mai fassara: Saminu Alhassan)