Ma’aikatar kudi da ta albarkatun ruwa ta kasar Sin, sun ware kudin Sin yuan RMB miliyan 55, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 7.75, don dawo da kayayyakin adana ruwa da suka lalace a lardunan Gansu da Qinghai, bayan girgizar kasa mai karfin maki 6.2 da ta afku a yammacin ranar Litinin.
Adadin wadanda suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.2 da ta afku a lardin Gansu dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin ya kai 782 a Gansu, inda ya zuwa karfe 9 na safiyar Larabar, adadin wadanda suka mutu ya kai 113.
Bayanai na cewa, girgizar kasar ta kashe mutane 21 a lardin Qinghai. Ya zuwa karfe 4 na yammacin yau, an samu rahoton jikkatar mutane 198 a Qinghai sakamakon bala’in, yayin da wasu 13 suka bace. (Ibrahim Yaya)