‘Yan majalisar dokokin Jihar Zamfara sun kori kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar, Alhaji Abdulmalik Gajam daga zauren majalisar yayin gabatar da kasafin kudin 2024 da gwamna Dauda Lawal ya gabatar a yau Alhamis.
‘Yan majalisar sun ce hakan ya biyo bayan kin amsa gayyatar kwamishinan da majalisar ta yi masa a baya sau uku a jere.
- Tinubu Ya Sake Bullo Da Shirin Ciyar Da Dalibai A Makarantu
- Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓen Kano, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
Dan majalisa mai wakiltar Gummi, Bashir Aliyu ya gabatar da kudiri kafin a fara gabatar da jawabi ya jawo hankalin majalisar kan rashin da’ar da kwamishinan Abdulmalik Gajam yayi musu.
Ya ce majalisar dokokin na da damar gayyato duk wani mutum musamman wadanda ke rike da mukamai a gwamnati amma kwamishinan ya ki ya amsa gayyatarsu har sau uku kuma ya ki yin bayani ga majalisar.
Da yake bayar da gudunmuwa a kan kudirin dan majalisa mai wakiltar Maradun ta daya, Faruk Dosara ya yi kira ga majalisar da su amince a kan kwamishinan da ya fice daga zauren majalisar.
A hukuncin da ya yanke, kakakin majalisar, Bilyaminu Ismaila Moriki ya umarci bangaren da ke kula da sandar majalisar da su kori kwamishinan daga zauren majalisar.