Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ya bayyana cewa duniya ba za ta iya ci gaba da gudanar da harkokin kudade da ake ba da bashi da ruwa mai yawa ba. Kana ya ce wannan ne ya sa Nijeriya ta karkata ga cibiyoyin kudi na Musulunci.
Ministan ya ce matsalolin da aka sama na ma’adanai sun sa farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi, sannan kuma ya sa an kara kudin ruwa wajen amsar bashi.
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Amincewa Da Yarjejeniyar Dakile Bazuwar Bindigogi Muhimman Mataki Ne Da Sin Ta Dauka Don Ingiza Tsaron Duniya
Ministan ya bayyana hakan ne a wurin wani taro da hukumar kula da harkokin kasuwanci (SEC) da hukumar kula da kudade ta Musulunci (IFSB) suka shirya a Abuja.
Da yake jaddada illar tasirin kudaden ruwa mai yawa, ministan ya ce sun san ba zai yiwu a sami kudaden da ake bukata don ci gaban kasa da kayayyakin more rayuwa da ma ayyukan jin dadin jama’a ba, idan aka ci gaba da amfani da tsarin kudaden ruwa mai yawa.
Mininstan ya zayyano ababen more rayuwa kamar ilimi da kiwon lafiya a matsayin wasu muhimman wuraren da ke fama da matsanancin basuka.
Edun ya ja hankali game da tallafin dala miliyan 30 na baya-bayan nan daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da aka sadaukar don ayyukan sauyi da aka amince a Nijeriya.
Ya ce, “An bayar da wannan lamunin ne ta hanyar ka’idojin kudi na Musulunci, domin sauyin yanayin albarkatun da ake da su. A bayyane yake, a wannan lokaci kudade suna tare da masu gudanar da harkokin kudi na Musulunci.”
Edun ya ce a matsayinsa na ministar kudi, gwamma ya bi wadannan kudade.
Ya bukaci a zurfafa fahimta da amfani da kudaden a bankunan Musulunci, yana mai daukansu a matsayin hanyan hada-hadar kudade da ake samun ci gaba wanda IFSB ta amince da su..