Gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba da umarnin biyan albashin watan Disamba ga dukkan ma’aikatan jihar da takwarorinsu a ƙananan hukumomi a wani mataki na ganin ma’aikatan Jihar Gombe sun kimtsa, kuma su yi bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara cikin jin daɗi da annashuwa.
Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan YaÉ—a Labarun Gwamnan Jihar Gombe shine ya sananar da wannan matakin, inda gwamnan ya umarci ma’aikatar kudi ta jihar da ta tabbatar kowani ma’aikaci da ‘yan fansho sun samu albashinsu a watan Disamba a kan lokaci.
- Wakilin Sin: Ya Dace A Daidaita Batun Kiyaye Zaman Lafiya Na AU Ta Hanyoyin Afirka
- ’Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-17 Sun Gama Aiki A Wajen Kumbo A Karon Farko
Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da kyautata jin daɗin ma’aikata ta hanyar biyan albashi da sauran haƙƙoƙinsu cikin gaggawa.
Ya na da kyau a sani cewa Jihar ta Gombe tana ci gaba da sauƙe nauyin da ya rataya a wuyanta yadda ya kamata game da haƙƙoƙin ma’aikatanta kama daga biyan albashi akan kari da kuma ci gaba da bada tallafin Naira dubu goma-goma ga kowane ma’aikaci a jihar. Wannan karimci na gwamnan yana ƙara ci gaba, yayinda a wassu jihohin ba a samun ko kwatankwacin haka.
Gwamna ya miÆ™a gaisuwarsa da fatan alheri ga al’ummar jihar tare da yi wa al’ummar Kirista fatan yin bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara lafiya.