Kamfanin mai ta kasa (NNPC) ta sanya hannun jarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin TotalEnergies domin fara amfani da fasahar gano abubuwa ta nau’in iskar gas marar launi ko marar sunsuno da ke konewa wato ‘methane’.
Fasahar dai an fi saninta da kwarren manhajar haske da ke haskaka muhalli (AUSEA) domin gano nau’ikan abubuwan da ke cikin teku daban-daban.
- Gwamnati Za Ta Samar Da Tsaro A Filayen Hakar Ma’adanai —Alake
- Mahaifiyar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Dogara Ta Rasu, Ta Na Da Shekara 103
Wannan matakin duk na daga cikin yunkurin kamfanin TotalEnergies na zuba hannun jarin dala biliyan 6 a Nijeriya cikin shekaru masu zuwa.
Kamfanin makamashin zai maida hankali ne wajen aiki ruwa mai zurfi da samar da iskar gas da taimaka wa Nijeriya wajen habaka sashin hako gas da kuma kyautata yanayin muhalli.
Sanya hannun zai taimaka wa Nijeriya wajen amfani da manhajar AUSEA a ayyukanta da suka shafi teku domin gano matakin methane da zai taimaka wa dumamar yanayi.
A madadin NNPC, mataimakin shugaba a kamfanin bangaren teku, Oritsemeyiwa Eyesan, da daraktan gudanarwa na shugaban kamfanin TotalEnergies a Nijeriya, Matthieu Bouyer, sune suka sanya hannun a madadin bangarorin biyu, a karkashin sanya idon shugaban kamfanin mai ta kasa Mele Kyari, da shugaban kamfanin TotalEnergies, Patrick Pouyanné.
A bangarensa, shugaban kamfanin TotalEnergies, Patrick Pouyanné, ya ce, kamfanin za ta taimaka wa NNPC da fasahar da zai taimaketa wajen bunkasa aiki da kyautata fitar da mai da iskar gas.