Gwamnatin jihar Bauchi ta bayar da kyautar naira miliyan 100 ga ƙungiyoyin ‘yan Bijilante da ‘yan Banga domin nuna godiya da jinjina kan irin kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali musamman wajen kare dazukan da suke jihar daga aikace-aikacen ‘yan bindiga.
Gwamnan jihar Bala Muhammad shi ne ya sanar da wannan matakin a ranar Asabar lokacin da ya amshi bakwancin mambobi da shugabannin ƙungiyoyin ‘yan Bijilante da ‘yan Banga da suka kai masa ziyara ta musamman a gidan gwamnatin jihar.
- Haaland Ya Zama Gwarzon Dan Wasan Duniya Na BBC A Bana
- Gwagwarmayar Neman Takardar Naira: Ina Tsabar Kudin?
Gwamna Bala ya buƙaci ‘yan bijilante ɗin da su tabbatar da yin amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da suka dace tare da sayan kayayyakin da suka dace da za su taimaka musu wajen inganta ayyukansu.
Ya ce, tallafin zai ɗauki tsawon lokaci na taimaka musu wajen bada nasu gudunmawar wajen tabbatar da daƙile aikace-aikacen ta’addanci da ‘yan ta’adda a faɗin jihar.
A cewarsa, zaman lafiyan da jihar Bauchi ke mora, ya taimaka wajen janyo hankalin masu zuba hannun jari domin su zo jihar wajen zuba hannun jari a ɓangarori daban-daban na cigaban tattalin arziki.
Gwamnan ya bayar da tabbacin gwamnatin jihar a ƙarƙashinsa na cigaba da taimaka wa hukumomin tsaro ciki har da ‘yan sa-kai wato ‘yan ƙato da gora domin kyautata zaman lafiya a jihar.
Ya ce, sabuwar ma’aikatar kula da tsaron cikin gida za ta cigaba da maida hankali wajen fito da tsare-tsaren da suka dace na kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.
A nasa ɓangaren, kwamanda janar na ƙungiyar mafarauta, Aliyu Umar Shayi, ya ce, ƙungiyarsa na aiki ƙungiyoyin ‘yan bijilante sama da 70 a sassa daban-daban na jihar da suke bada nasu gudunmawar wajen kyautata zaman lafiyan jihar.
Shayi ya nuna godiyarsu ga irin taimako da goyon bayan da gwamnan jihar ke basu wajen gudanar da nasu ayyukan yadda ya kamata a matsayinsu na ‘yan sa-kai.