Gwamnatin Zamfara ta ware Naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 don inganta gidajen Rediyo da Talabijin da Kamfanin Jarida na Legacy mallakar gwamnati.
Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mannir Haidara, ne ya bayyana hakan a Gusau ranar Litinin bayan kare kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamitin kudi da kasafi na majalisar dokokin jihar Zamfara.
- Gwamnan Zamfara Ya Gabatar Da Kasafin N432.5b Shekarar 2024
- ‘Yan Majalisar Dokokin Zamfara Sun Kori Kwamishinan Kasafin Kudi Daga Zauren Majalisar
LEADERSHIP HAUSA, ta ruwaito cewa a ranar Alhamis ne Gwamna Dauda Lawal ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 423.5 ga majalisar don neman amincewa da shi.
Haidar ya ci gaba da cewa, za a aiwatar da ayyukan inganta kafafen yada labaran jihar a karkashin manufar Gwamna Dauda Lawal na farfado da harkar yada labarai a jihar.
“Kamar yadda muka sani, ma’aikatar yada labarai ce ke da alhakin kula da kafafen yada labarai a jihar, mun bullo da ayyuka daban-daban don inganta masana’antar watsa labarai ta jiha bisa kyawawan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Gwamna Lawal,” in ji shi.
Haidar ya ci gaba da cewa, sauran hukumomin da za su ci gajiyar wannan aikin na zamani (Digital) sun hada da Hukumar Tace Fina-finai ta Zamfara da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA).
“Gwamnatin jihar za ta aiwatar da gyaran gaba daya tare da samar da kayan aiki na zamani ga gidajen rediyon Zamfara AM da Gidan Rediyon FM na Gold City da Kamfanin Jarida na Legacy na Jihar da kuma Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar.