Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a Abuja ranar Talata, ta ce, Tinubu ya bada umurni ga jami’an tsaro da su gaggauta shiga yankin da lamarin ya faru domin cafke wadanda suka aikata wannan mummunan lamari.
- An Kashe Mutane 700, An Lalata Kauyuka 50 Cikin Wata 3 A Mazabata — Sanata
- Gwamnatin Sakkwato da Wamakko Sun Tallafa Wa Mutane 66 Da Sojoji Suka Ceto
Shugaban ya kuma ba da umarnin a gaggauta kai kayayyakin agaji yankin, da kuma ba da agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
A yayin da yake jajantawa gwamnati da al’ummar Filato, shugaba Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, wadanda suka aikata wannan laifi za a zakulo su kuma za a hukunta su.