Cibiyar binciken fasahar bayanai da sadarwa ta CAICT, wadda ke karkashin ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin, ta ce adadin wayoyin salula da kamfanonin kirar su suka fitar a kasar ya karu da kaso 34.3 bisa dari bisa na makamancin lokacin bara, inda adadinsu ya kai sama da miliyan 31.21 a watan Nuwamba.
Cikin adadin, wayoyin dake aiki da fasahar 5G ne mafiya yawa a watan na Nuwamba, inda adadinsu ya kai miliyan 27.09, karuwar da ta kai kaso 51.2 bisa dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.
- Jawabin Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Na Murnar Sabuwar Shekarar 2024
- Shugaban Kasar Sin Zai Gabatar Da Jawabin Maraba Da Sabuwar Shekarar 2024
Cibiyar CAICT ta kara da cewa, a watan na Nuwamba, wayoyin salula kirar kamfanonin gida sun ci gaba da kasancewa kan gaba a kasuwannin kasar Sin, inda kamfanonin na gida suka fitar da karin kaso 26.5 bisa dari bisa na makamancin lokacin bara, adadin da ya kai miliyan 25.44.
Har ila yau, adadin wayoyin salula da kamfanonin suka fitar cikin watanni 11 na farkon shekarar nan mai karewa, sun karu da kaso 7.1 bisa dari, inda adadinsu ya kai miliyan 261. (Saminu Alhassan)