Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya yi wa fursunoni 39 da ke zama a gidan yari daban-daban a fadin jihar afuwa.
Yahaya ya bayyana haka a wani jawabi da ya rabawa al’ummar jihar a ranar Litinin a Gombe, a wani bangare na bukukuwan sabuwar shekara.
Gwamnan ya bayyana cewa yin afuwa ga fursunonin wani bangare ne na bikin sabuwar shekara da kuma bai wa fursunonin damar canja yanayin yadda suke rayuwa kamar yadda kowa ke rayuwa.