Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Iran Ebrahim Raisi, dangane da munanan hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar.
Xi ya ce, ya kadu matuka da samun labarin munanan hare-haren ta’addanci da aka kai a yankin Kerman na kasar Iran, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dama.
- Kasar Sin Ta Zama Babbar Kasa A Fannin Kiyaye Ikon Mallakar Fasaha Kuma Muhimmin Jigo A Fagen Kirkire-kirkire A Duniya
- Harbin Kasar Sin Ya Samu Bunkasuwar Yawon Shakatawa A Lokacin Hutun Murnar Sabuwar Shekara
A madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, shugaba Xi ya mika ta’aziyyar wadanda abin ya shafa, da nuna janjantawa ga wadanda suka jikkata da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’in ta’addanci, tana kuma yin Allah wadai da hare-haren ta’addanci, tana kuma goyon bayan kokarin da kasar Iran ke yi wajen kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a kasar
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba yi Alhamis din nan cewa, kasar Sin ta yi kakkausar suka kan harin ta’addanci da aka kai a kasar Iran, tare da nuna goyon baya ga kokarin Iran na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar. (Ibrahim)