Wasu masu garkuwa da mutane domin binyan kudin fansa, sun sako ‘yar fasto Daniel Umaru, ‘yar kasa da shekara 13, biyo bayan biyan kudin fansa, a garin Kwarhi a karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.
Sai dai ba a bayyana yawan adadin kudaden da aka biya, domin ceto rayuwarta ba.
- Zargin Badakalar 1.85bn: Buratai Zai Maka ‘Sahara Reporters’ A KotuÂ
- Hawan Nassarawa: Sarkin Kano Ba Zai Ziyarci Gidan Gwamnatin Kano Ba
Rahotanni, sun tabbatar da cewa ba ranar Asabar ne ‘yan uwa da abokan arziki, suka gudanar da jana’izar ‘yan uwan yarinyar biyu da masu garkuwa da mutanen suka kashe, lokacin da suka je sace yarinyar.
Dama dai a ranar 7 ga watan Yulin 2022 ne, rahotanni sukace wasu mutane sun shiga gidan Fasto Daniel Umaru, suna harbe-harben bindigogi, inda sika kashe ‘ya’yansa biyu da garkuwa da ‘yarsa ‘yar shekaru 13, yanzu haka dai faston na ci gaba da karban magani a asibiti.
Majiya daga iyalan yarinyar sun tabbatar da cewa mutanen da suka yi garkuwa da yarinyar sun sako ta, biyo bayan biyan makudan kudade, sai dai majiyar bata bayyana yawan kudaden ba.
Tace “mun biya kudade da yawa, kafin masu garkuwa da ita, su sako mana ita a ranar Asabar da yamma, bayan an gudanar da jana’izar ‘yan uwanta biyu a harabar cocin EYN a Kwarhi.
“A yanzu haka dai, ita da babanta likitoci na kokarin ceto rayuwarsu a asibitin Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, biyo bayan raunukan da maharan suka ji musu” in ji majiyar iyalin Faston.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sako yarinyar, DSP Sulaiman Ngoroji, shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce tuni yarinyar ta koma gida.