A jiya ne, aka fara aiki da sabuwar na’ura mai kwakwalwa da kasar Sin ta tsara ta kuma kera da kanta, da ake kira Origin Wukong a kamfanin Quantum Computing Technology (Hefei) Co., Ltd da ke lardin Anhui na gabashin kasar Sin.
A cewar masu bincike, na’urar tana amfani da fasahar Wukong ne, tana kuma amfani da majiyar tattara bayanai mai karfin qubit 72. A halin yanzu ita ce na’ura mai kwakwalwa ta zamani da kasar Sin ta kera kuma mafi ci gaba da za a iya amfani da ita wajen tsarawa da kuma iya isar da mafi kyawun bayanan kwamfuta.
- Bashin Amurka Ya Kai Sabon Matsayi Wanda Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasar
- Dalibin Kasar Benin: Ina Da Burin Kai Fasahohin Aikin Noma Na Kasar Sin Zuwa Kasar Benin
Mataimakin darektan Cibiyar binciken Injiniyan Kwamfuta ta Quantum ta Anhui, Kong Weicheng ya bayyana cewa, an hada kwamfutar tare da tsarin kula da kididdiga na zamani wanda ke kara ingancin aiki na kwamfutar sau da dama
Jia Zhilong, mataimakin darektan Anhui Quantum Computing Chip Provincial Key Laboratory ne a karkashin cibiyar binciken injiniyan Kwamfuta, ya ce matattarar bayanan Wukong na da qubits 198, wanda ya kunshi qubits 72 da kuma qubits 126.
Sun Wukong dai wani Basine ne a tatsuniyar kasar Sin, wanda ke da fasahar rikidewa zuwa nau’o’in daban-daban har guda 72, abin da ke nuna karfi da ingancin na’ura mai kwakwalwar.(Ibrahim)