Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake wa ma’aikatar jin kai da yaki da fatara na karkatar da kudaden jama’a.
Za a gudanar da binciken ne don tabbatar da sahihanci zargin da ake yi wa ma’aikatar na karkatar da kudi har Naira Miliyan N585.
- 2024: Gidauniya Ta Tallafa Wa Zawarawa Da Kayan Masarufi Da Kudi A Kaduna
- Trump Ya Daukaka Kara Kan Hukuncin Hana Shi Shiga Zabe
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ministar harkokin jin kai, Betta Edu, ta fuskanci suka bayan wata takarda da aka fallasa mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Disamba, 2023, ta bayyana cewa, ta umurci babban akanta na kasa, Oluwatoyin Madein da ya tura Naira miliyan N585 zuwa wani asusun sirri, wacce ma’aikatar ta yi ikirarin cewa, a halin yanzu, asusun sirrin shi ne ma’ajiyar kudade da za a kula da ayyukan tallafi na kungiyoyin masu rauni.
Wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Lahadi a Abuja mai dauke da sa hannun ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ta ce, shugaban kasar ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike don tabbatar da sahihanci da ingancin bayanan da aka rahoto kan wannan zargin da ake yi wa ma’aikatar jin kai nan take.